Maryam Sanda: Ashe Bilyaminu ba yaron tsohon Shugaban PDP bane

Maryam Sanda: Ashe Bilyaminu ba yaron tsohon Shugaban PDP bane

- Labarin Maryam Sanda ya dauki wani sabon salo yanzu

- Ashe Marigayi Bilyaminu Bello ba dan babban gida bane

- Dangin ta sun Marigayin ya gaje kayan ta ya kuma fusata ta

Kwanan nan aka samu wata Baiwar Allah mai suna Maryam Sanda da ake zargi ta hallaka mijin ta har lahira saboda tsabar kishi. Sai dai yanzu haka mu na cigaba da samun wasu bayanai game da abin ya rika wakana a lokacin zaman aure na su tun daga soyayyar da su kayi a Makarnta.

Maryam Sanda: Ashe Bilyaminu ba yaron tsohon Shugaban PDP bane
Dangin Maryam Sanda sun kare 'Yar uwar su

Asali dai kamar yadda mu ka samu labari Bilyaminu ba ‘Dan Bello Halliru bane, sai da ‘Dan uwan sa ne kurum. Kuma dangin Bilyaminu ba su da kudi na wani a zo a gani. Bari ma dai Mahaifiyar Maryam Sanda ce tayi kusan komai a bikin har ta kama masu katafaren gida a Maitama.

KU KARANTA: Za ka iya auren Maryam Sanda idan ta tuba?

Ana ma cewa har sai da ta kai motar da aka ba Maryam kyauta, Mijin na ta lokacin ya maida ta tamkar ta sa. Ya nemi ya gaje kusan komai na ta. Nan ta fahimci cewa ba su da wani hali kamar yadda yake fada, kuma yana bin wasu ‘yan mata ko da dama ya taba wani gajeren aure.

A cewar dangin Maryam Sanda, ta kai lokacin da sai da Maryam ta nemi a sake ta saboda ta ga abin Marigayin yana cigaba da tabarbarewa. A daren da abin ya faru dai su ganin Bilyaminu ya fusata ta hara abin tsaustayin ya kai ga yayi asarar jini sosai. Yanzu haka dai Maryam tana tsare a gidan Yari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng