Dalilin da yasa yin wasan Hausa da yaren turanci keda muhimanci - jaruma Fati SU
Jarumar wasan Hausa Fati SU ta ce shawarar da abokan sana'ar ta suka yanke na yin shiri da yaran turanci abu ne mai muhimmanci kuma tayi maraba da hakan.
Fati ta bayyana haka ne yayin wata tattaunawa da gidan jaridar Premiumtimes ranar Asabar.
Fati ta ce "Na san ba wai turanci muka iya sosai ba amma idan muna yi shiri da turanci hakan zai bamu damar govewa da yaren".
Da take yin tsokaci a kan rata ta fuskar kayan aiki da kamfanin shirya fina-finai na kudu da yayi wa kamfanin Kannywood, ta ce "Eh haka ne amma mu ma fa yanzu muna kokari kuma yin fina-finai cikin harshen turanci zai kara sada mu da manyan kamfanoni da suka fi mu gogewa kuma mu ma jaruman mu zasu fara samun kyauta daga kungiyoyin shirya fina-finai ta kasa".
DUBA WANNAN: Kashe-kashen Numan: Matasan Fulani sun fusatta, sunce zasu dauki mataki
Fati ta bayyana cewar su 'yan koyo ne da suke son kara fadada yada al'adar bahaushe ta hanyar yin shiri da yaren turanci. Yin hakan ma zai kara mana magoya daga dukkan kabilu daga fadin Najeriya.
Fati ta ce shirin ta na gaba "There is a way" zai fito nan bada dadewa ba kuma za a fara nuna shi a sanima watan Disamba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng