Labari da duminsa: Kotu ta bada umarnin tsare Maryam Sanda a gidan yari

Labari da duminsa: Kotu ta bada umarnin tsare Maryam Sanda a gidan yari

- Matar da ake zargi da kashe mijinta ta hanyar caccaka masa wuka ta bayyana gaban wata babban kotu a Abuja

- Maryam Sanda ta iso cikin kotun dauke da jaririyar su mai wata 7 da kuma Al-Qurani mai girma a hannun ta

- Maryam ta musanta zargin aikata kisan amma amma Alkali ya bada umurnin a tsare ta gidan yari kuma ya dage sauraron karar zuwa ranar 7 ga watan Disamba

Maryam Sanda, matar ta ake zargi kashe mijin ta, Bilyamin Muhammed Bello, ta hanyar caccaka masa wuka bayan ganin wani sakon waya da wata budurwar ta aika zuwa wayar sa ta hannu, ta gurfana gaban kotu bisa tuhumar aikata laifin kisa.

Maryam ta rushe da kuka yayin da ta isa cikin kotun rike da jaririyar su mai wata 7 kacal a duniya, sannan ta rufe fuskarta da wani koren kyalle domin gudun daukan hoton ta.

Kafin fara shari'ar, Maryam, ta bude littafin alqur'an mai girma tana karantawa.

Labari da duminsa: Kotu ta bada umarnin tsare Maryam Sanda a gidan yari

Labari da duminsa: Kotu ta bada umarnin tsare Maryam Sanda a gidan yari

Maryam ta dauki rantsuwar fadawa kotu gaskiya kamar yadda yake shimfide a doka sannan ta musanta aikata laifin da ake ta zargin ta da aikatawa.

DUBA WANNAN: Kimanin mutane 40,000 ne ke neman aikin malanta a Jihar Kaduna

Bayan Maryam taki amincewa da aikata laifin kisan Bilyamin, lauyan ta, Hussein Musa, ya roki kotu ta bar wacce yake karewa a hannun 'yan sanda, saidai mai shari'a, Yusuf Halilu, ya umarci da a cigaba da tsare Maryam a gidan yari na Suleja yayin da ya daga sauraron shari'ar zuwa 7 ga watan Disamba.

A karshen satin ne da ya gabata ne labarin kisan Bilyamin da matar sa Maryam ta aikata ya mamaye kafafen yada labarai. Bilyamin Muhammed Bello da ne ga tsohon shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Halliru Bello.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel