Masha Allah, Mutumin da matarsa ta caccaka ma kwalba na samun sauki
Sauki ya fara samuwa ga Malam Bilyaminu, mutumin nan da matarsa Murjanatu ta caka masa kwalba a kai, wanda daga bisani kuma ta soka masa shi a kirjinsa, inji rahoton Rariya.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito a yanzu dai an samo ran Bilyaminu, inda aka hange shi yana kwance akan gadon asibiti yana shan ruwan leda, tare da bandeji a jinkinsa.
KU KARANTA: An sake kwatawa: Uwargida ta caccaka ma Maigida kwalba a kirjinsa, yana nan rai fakwai, mutu fa kwai
Shi dai wannan mutumi ya gamu tasku ne a ranar Laraba 22 ga watan Nuwamba, inda da sanyin safiya matarsa Murjanatu ta nemi ta je caji ofis don duba wani dan uwanta da aka kama, inda shi kuma ya hana ta.
Sai dai ashe hakan bai yi ma matar dadi ba, inda ta mamaye shi ta buga masa kwalbar a kai, yayin dayake yunkurin dagowa kuma ta caka masa a kirji.
Amma zuwa yanzu, Yansanda sun samu nasarar kama Murja, kuma ana gudanar da bincike, wanda da zarar an kammala wannan bincike za’a mika ta gaban kuliya manta sabo.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng