Cikin Hotuna: Jerin mata mawaka 4 da suka kere sa'anninsu diban kudi a shekarar 2017

Cikin Hotuna: Jerin mata mawaka 4 da suka kere sa'anninsu diban kudi a shekarar 2017

A yau Legit.ng ta bakada cikin fagen nishaɗi inda ta kawo muku jerin mata 4 da suke sana'ar waka a duniya, wanda binciken ya bayyana cewa sun kere sa'anninsu na duniya kwasar kudi a fagen sana'ar ta su a shekarar 2017.

Beyonce Giselle Knowles-Carter
Beyonce Giselle Knowles-Carter

Kamar yadda jaridun kasashen ketare musamman mujallar Forbes da kuma na nan gida Najeriya suka wallafo, shahararriyar mawakiyar nan mai sunan Beyonce Giselle Knowles-Cater, ita ce sahun farko na kwasar kudi a shekarar 2017.

Mawakiyar ta samu zunzurutun kudi da suka tasar ma Dalar Amurka miliyan 105 kamar yadda mujallar ta Forbes ta fitar a ranar Litinin din da ta gabata.

Adele Laurie Blue Adkins
Adele Laurie Blue Adkins

Sai kuma mawakiyar kasar Amurka mai shekaru 29, Adele Laurie Blue Adkins, ta biyo bayan Beyonce da kwasar kudi na Dalar Amurka Miliyan 69.

Taylor Alison Swift
Taylor Alison Swift

Shahararriyar mawakiyar nan wadda ake mata lakabi da kullum yarinya take dawowa wato Taylor Alison Swift, mai shekaru 27 a duniya, ta hau mataki na uku da kudi na dalar Amurka Miliyan 44., wadda a shekarar da ta gabata ita ta ja ragamar mata mawaka da suka fi kowa kwasar kudi da dalar Amurka Miliyan 170.

Ana sa ran samun mawakiya Taylor zai linku cikin watanni 12 masu gabatowa sakamakon wasu sababbin wakoki da za ta saki wadanda za su kece raini a duniyar waka.

KARANTA KUMA: Bamu da zababben dan takarar shugabancin Najeriya a zaben 2019 - Kasar Amurka

Celine Marie Claudette Dion
Celine Marie Claudette Dion

Tsohuwar mawakiyar nan ta kasar Canada, Celine Marie Claudette Dion mai shekaru 49 a duniya, ita ce da hau mataki na hudu a jerin mawakan da kudi wadanda suka tasar ma Dalar Amurka Miliyan 42, wanda masana ke cewa, mutuwar mijinta Rene Agngelil watan Janairun shekarar 2016, ita ta janyo mata tsaiko a harkar sana'ar ta ta.

LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng