Asibiti ta tsare mai jego da danta har tsawon watanni 4 bisa rashin biyan kudin tiyata
- Wani saurayi mai suna Chibugo Duru ya tsere ya bar budurwarsa a asibiti bayan ta haifa masa da
- Duru dai ya tsere ne domin ya kasa biyan kudin tiyata Naira 215,000 da akayi wa budurwar tasa wajen haihuwa
- Hukumar asibitin sunce sunyi mata rangwamen kudin gado da abincin da suka ciyar da ita na tsawon watanni uku amma sai an biya su kudin tiyatar kafin su sallame ta
Haihuwa dai abin farin ciki ne da murna sai dai an samu akasin haka yayinda wata budurwa mai shekaru 21 a duniya, Blessing Agbor ta haifi yaron ta. Hassali ma ita haihuwan nata ya jawo mata tozarta ne da kunyata.
Watanni 4 da suka wuce Agbo ta haifin danta ta hanyar tiyata a wata asibiti mai suna God Cures Hospital da ke Legas amma asibitin sun rike ta tare da danta domin ita da saurayinta, Chibugo Duru sun kasa biyan Naira 215,000 kudin tiyatar.
Majiyar Legit.ng ta tataro cewa a halin yanzu, Uban yaron wato Duru, ya tsere ya bar Uwar tare da dan da ta haifa a asibitin da ke Ilogbo a Unguwar Ojo da ke Legas.
Mr Duru mai shekaru 27 yayi magana da Jaridar Punch ta wayar salula inda ya fada musu cewa ya bar Agbo da dan su ne domin ya kasa samo kudin ta zai biya a sallame su daga asibitin.
DUBA WANNAN: Malamai 51 sun fadi jarrabawar malanta a Legas – TRCN
Ya kara da cewa a cikin watan Yuli aka kira shi a waya kuma aka sanar dashi cewa budur tasa tana nakudu kuma tana bukatan tiyata a kan kudi Naira 245,000, yace ya nemi ragi amma asibitin basu amince ba saboda haka yace ayi tiyatar idan ya dawo daga tafiyar da yayi zai biya kudin.
Bayan dawowar sa, ya bisa Naira 30,000 kuma kwatsam sai ya rasa aikin sa, hakan ne yasa bai samu inda sai samo sauran kudin ba.
Wani jami'i daga asibitin ya shaida wa Jaridar Punch cewa sunyi tiyatar ne saboda tausayi kuma su suke ciyar da uwar da danta har na tsawon watanni 3, ya ma kara da cewa sunyi mata saukin kudin gado N1,500 wadda ya kamata tana biya a kullum, kudin tiyatar ne kawai suka ce a biya su.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng