Dangote yayi ɓarin kuɗi a bikin ƙaddamar da littafin marigayi Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi I

Dangote yayi ɓarin kuɗi a bikin ƙaddamar da littafin marigayi Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi I

An tara makudan kudi da suka haura naira miliyan 70 a bikin kaddamar da littafin tarihin marigayi Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi na farko, kakan Sarkin Kano na yanzu, Muhammadu Sunusi II.

Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito babban mai kaddamarwa, Alhaji Aliko Dangote ne ya fara bude taro, inda ya siya kwafin littafin akan naira na gugan naira, har miliyan 10.

KU KARANTA: Neman kudin aure: Wani Matashi yayi garkuwa da budurwarsa, da nufin amsan kudin fansa

Shima Lamidon Adamawa, Alhaji Muhammad Mustapha ya samu halartan taron, inda ya bayyana littafin a matsayin wani tuna baya ga irin kyawawan halayen tsohon Sarki, Muhamamdu Sunusi I.

Dangote yayi ɓarin kuɗi a bikin ƙaddamar da littafin marigayi Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi I
Bikin ƙaddamar da littafin marigayi Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi I

A nasa jawabin, Wazirin Adamawa, Alhaji Atiku Abubakar ya yaba ma kokarin da Sarkin Kano yayi na raya tarihin Kakansa, tare da bayyana marigayin a matsayin abin koyi. sa’annan ya koka kan yadda aka cire karatun tarihi daga manhajan karatu a makarantun Najeriya.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Atiku yana fadin “Najeriya zata gyaru, idan shuwagabannin zamanin nan suna kwaikwayo da shuwagabannin da suka gabata, musamman wadanda suka yi abin alheri ga jama’ansu.”

Dangote yayi ɓarin kuɗi a bikin ƙaddamar da littafin marigayi Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi I
littafin marigayi Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi I

Daga karshe Atiku ya bayyana littafin a matsayin wata hanyar bude idanu ga yan Najeriya, kuma yayi kira ga gwamnati data mayar da ilimin tarihi cikin manhajar karatu a makarantun Najeriya.

Kimanin gwamnoni biyar tare da Sarakuna goma ne suka halarci taron kaddamar da littafin tarihin marigayi Sarkin Kano, mai taken ““Power and Piety Life and Legacy of Sir Muhammadu Sanusi I” wanda Muhammed Rabiu Umar da Ahmed Tijjani Abubakar suka rubuta.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng