Yan majalisa 2 kacal da PDP ke dasu a jihar Nasarawa zasu sauya sheka zuwa APC – Kakakin majalisa

Yan majalisa 2 kacal da PDP ke dasu a jihar Nasarawa zasu sauya sheka zuwa APC – Kakakin majalisa

Kakakin majalisan dokokin Jihar Nasarawa, Ibrahim Balarabe Abdullahi, ya ce sauran mambobi guda biyu da suka rage a jam’iyyar PDP zasu sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.

Abdullahi ya fadi haka ne jiya a Lafia, inda yace, an kammala shirye-shirye kan mambobi biyu masu wakiltan Akwanga ta yamma da Doma ta kudu - Peter Umbuchu da Muhammed Okpede don sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.

“Mun kammala shawara tare da su mun kuma fahimci juna. Yanzu haka muna shirin aza kwanan wata don sauya sheka,” a cewar shugaban majalisan.

Yan majalisa 2 kacal da PDP ke dasu a jihar Nasara zasu sauya sheka zuwa APC – Kakakin majalisa
Yan majalisa 2 kacal da PDP ke dasu a jihar Nasara zasu sauya sheka zuwa APC – Kakakin majalisa

Abdullahi ya ce jam’iyyar PDP tana da mambobi guda biyar a lokacin da aka kaddamar da majalisan a shekara 2015, amman cewa uku daga cikin su sun bar jam’iyyar a shekara da muke ciki saboda jam’iyyar APC ta janyo hankalinsu ta hanyar matakai dsa gwamnatin take daukawa don cigaba.

KU KARANTA KUMA: Wallahi ko kadan ban yi niyyar kashe masoyina uban 'yata ba - Inji Maryam Sanda

Ya kayyade cewa majalisan zata cigaba da goyon bayan manufofin alkhairi da shirye-shiryen gwamna Al-Makura don cigaban jihan.

Ana iya tunowa a baya cewa Godiya Akwashiki, daga Nassarawa-Eggon ta yamma; Moluku Aga, Nassarawa-Eggon ta gabbas; da Muhammed Alkali, Lafia ta arewa, kwanakin nan suka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC daga PDP.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng