Ta hallaka mijinta, yaron tsohon shugaban jam’iyyar PDP ta hanyar caka masa wuƙa a Al’auransa
Soyayya gamon jini ce amma inda kauna, inji hausawa, sai dai a nan, wani abin ban mamaki, tausayi da ban haushi ne ya faru a sakamakon bakar kishin da wata mata ke da shi.
Yaron tsohon shugaban jam’iyyar PDP, kuma tsohon ministan tsaro, Halliru Bello, mai suna Bilyamin Muhammed Bello ya gamu da ajalinsa ne ba a hannun kowa ba illa matarsa, matarsa ta sunnah.
KU KARANTA: Wata tsohuwa ýar shekara 87 ta gamu da fushin Kotu saboda safarar Tabar Wiwi
Ita dai wannan mata mai suna Maryam Sanda, wanda diya ce ga tsohuwar shugaban kamfanin ‘Aso Savings’, Hajiya Maimuna Aiyu ta hallaka Bilyamin ne ta sanyar caccaka masa wuka a wurare da dama a jikinsa.
Legit.ng ta ruwaito wannan rikici ya faru ne sakamakon zargin yana tarayya da wata budurwa ta daban da matar tasa ke yi ne, inda da fari sai ta fara cizan masa kunne, kuma yayi jinya a asibiti bayan an dinke kunnen.
Rahotannin sun bayyana cewa abokansa sun bashi shawarar daya bar gidan, amma ina, ajali yayi kira, a daren Asabar, 18 ga watan Nuwamba ne, Maryan ta sadada dakinsa dauke da wuka, bayan tag a wani wasikar kar-ta-kwana a wayansa daga wata budurwa, inda ta mamaye shi ta caccaka masa a baya, sa’annan ta sossoka masa a al’auransa.
Sai dai bayan aikata wannan danyen aiki ne sai hankalinta ya dawo jikinta, inda ta dauke shi ta garzaya da shi asibiti da kanta, a can ne yace ga garinku nan, ya cika, tuni aka yi mai jana’iza a garin Abuja. marigayi Bello da Maryam suna da ya daya.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng