Naira biliyan 150, bajat din jiha guda a Najeriya, aka sayi wannan hoton na Yesu Almasihu a gwanjon hotuna

Naira biliyan 150, bajat din jiha guda a Najeriya, aka sayi wannan hoton na Yesu Almasihu a gwanjon hotuna

Leonardo DaVinci, mai zane-zane da falsafa da kimiyya, wanda ya rayu a Italiya, kimanin shekaru 500 da suka shude, ya bar manyan zanunnuka na Yesu, da Kiristanci, da sahabbansa, da ma na mata haka a gari, kamar na Mona Lisa ko kuma Madonna, wata mata mai murmushi da hotonta yafi kowanne zane a duniya tsada.

Naira biliyan 150, bajat din jiha guda a Najeriya, aka sayi wannan hoton na Yesu Almasihu a gwanjon hotuna
Naira biliyan 150, bajat din jiha guda a Najeriya, aka sayi wannan hoton na Yesu Almasihu a gwanjon hotuna

A gwanjon hotuna na tarihi masu muhimmanci ga mutane, an sayar da hoton Yesu Al-Masihu a farashin da ya kai dala miliyan 400, kwatankwacin Naira miliyan dubu dari har da hamsin kenan. Kudin bajat din jiha kenan a Najeriya.

DUBA WANNAN: Kalli hotunan wadda ta tada wa jama'ar Najeriya hankali

Shi dai Yesu, a fadin wasu jama'ar, ya rayu ne a cikin Yahudawa, da ga wani Kafinta mai suna Yusufu, da matarsa Maryamu, wadda daga baya ake cewa ai ma wai shi dan wani ubangiji ne da ke zama a sama.

Wannan yasa ake son shi Yesun har ma shi Leo da Vinci ya zana hotonsa da ma na sahabbansa, wanda a yanzu masoya ke rububin saya domin tubarraki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

A fadin su dai masu son Yesu, shi yazo ne ya ceci jama'a daga wani bala'i da wai in sun mutu zasu iya fadawa, musamman idan basu so shi ba, kuma basu yarda shi daga sama aka yo cikinsa ba. Don wannan tsoron ne mutane da yawa ke bauta masa, musamman turawa, shekaru 2000 kenan.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng