Farashin mutan Najeriya a Libya na kamawa daga dala 400 zuwa abin da yayi sama, a wani rahoto
- A kasar Libya akwai 'yan Afirka bakar fatada yawa da suke kkarin tsallakawa Turai
- Tun rasuwar Ghaddafi aka sami baraka kan masu kokarin shiga teku don zuwa kasashen
- Ana bautar da ma sayar da mutane a kasashen yankin saboda babu hukumomi da ke kula
A kasar Libya, a sabon rahoto da CNN ta Amurka ta wallafa, ya nuna ta yadda ake cinikin mutane bakaken fata kamar bayi a kasar Libya ta arewacin Afirka.
Tun wafatin Ghaddafi ne dai aka sami karuwar zurarewar bakaken fata daga kudu zuwa hamada domin tserewa zuwa kasar Italiya ko sauran Turai.
A matsin tattali da Najeriya ta shiga, an sami karin masu kokarin zuwa turai don neman aiki, wasu kuwa don karuwanci.
DUBA WANNAN: Kasar Dubai zata aika 'yan sama jannati duniyar wata
Tafiyar tana da hatsari sosai, saboda kishirwa a hamada, da ma lumewa a teku, ga kuma azabtarwa da suke sha hannun iyayyen gijinsu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
A sabon bidiyo da gidan CNN na Amurka mai yada labarai ya nuna, sai gashi har cinikin jama'a ake yi, ana sayar dasu kamar shanu, ko bayi na zamanin da, farashinsu kuwa yana kamawa daga dala 400 abin da yayi sama. Kusan Naira dubu dari da hamsin kenan.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng