Matan jihar Edo 16 da suka dawo daga kasar Libya suna da juna biyu

Matan jihar Edo 16 da suka dawo daga kasar Libya suna da juna biyu

- Gwamantin jihar Edo tana tallafa matar da aka dawo da daga kasar Libya

- Faith Joseph ta fada wa yan jarida cewa ta fuskanci rayuwar kaskanci da wahala a kasar Libya

- Gwamnan jihar Edo Obseki ya samar matan wajen zama da albashi dan kula da kan su

Mata goma sha shida 16 daga cikin mata169 da gwamantin jihar Edo ta tarbe su bayan an dawo da su daga kasar Libya a ranar Laraba suna da juna biyu.

Mafi akasarin matan sun ki yi ma yan jarida magana duk da wasu a cikin su, sun dawo da kananan yara.

Gwamnatin jihar Edo ta tarbi mata 84 haifaffun jihar Edo da aka dawo da su daga kasar Libya.

Matar jihar Edo 16 da suka dawo daga kasar Libya suna da juna biyu
Matar jihar Edo 16 da suka dawo daga kasar Libya suna da juna biyu

Gwamnan jihar Edo Obseki ya samar matan wajen zama da albashi dan kula da kan su.

KU KARANTA : Za a samar wa mutane na’aurar gwajin Kanjamau a gida

Daya daga cikin matan mai suna Joseph Faith ta fadawa yan jarida cewa ta fuskanci rayuwar kaskanci da wahala Libya gwanda ta tsaya a Najeriya idan tana da aikin yi da ta kara zuwa kasar waje.

Ta ce tana son ta koma makaranta ta cigaba da karatu

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng