Hukumar yaƙi da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi ta kama yan shaye shaye 108 a Katsina
Hukumar fatauci da ta’ammali da miyagun kwayoyi NDLEA ta sanar da kama yan shaye shaye su 108 a jihar Katsina daga watan Satumba zuwa Nuwamba.
Daily Trust ta ruwaito hukumar tana fadin ta kama sama da kilo 101.71 na kwayoyi daban daban da tabar wiwi a cikin watanni ukun data bayyana.
KU KARANTA: Ana wata ga wata: Masu garkuwa da mutane sun fito da sabon salon karɓar kudin fansa a jihar Kano
Kwamandan NDLEA, reshen jihar Katsina, Maryam Sani ta bayyana haka cikin wata hira da tayi da manema labarai, inda tace hudu daga cikin wadanda aka kama mata ne, ii kuma daliban makarantun gaba da sakandari ne, sai wasu kanana yara su 3.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito kwamanda Maryam ta bayyana cewa cikin kayan mayen da aka kwace, kilo 43.5 tabar wiwi ce, sai kilo 48 daya hada da kwalaban Tramol, Exol, da Diazepam, kwalabe 497.
Daga karshe, Kwamanda Maryam ta koka kan karuwar matasa, mata da kananan yara cikin harkar shaye shaye, inda ta bukaci aiki tukuru da kuma goyon bayan jama’a dan magance matsalar.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng