Daular Larabawa mai birnin Dubai zata aika 'yan sama jannati duniya Mars, har ma suyi rayuwa a can
- A daular Larabawa, gwamnati ta ce zata fara aika mutane zuwa duniyar Mars Mai makwabtaka da tamu duniyar
- Dama chan Dubai ta yi kaurin suna wajen zamananci da wayewa
- Sauran kasashen larabawa dai har yau suna kashe kawunansu
Gwamnatin kasar Dubai, wato UAE, ta ayyana cewa, cikin shekaru dari masu zuwa, zata kafa wani sabon birni a sama, a wata duniyar daban da ba tamu ba.
A cewar gwamnatin dai, zuwa 2117, zasu kafa tasha da kauyuka da mutane zasu iya zama a birnin da zasu kafa karkashin gilasai.
A 2020 dai za'a fara wannan hobbasa, inda zasu tura 'yan sama jannati domin su gano yadda sammai suke, a kuma kafa sansani a kan wata.
DUBA WANNAN: Gwamnatin tarayya zata kara haraji a kan taba da giya
A wannan hobbasa dai, kasar UAE dama a yankin Larabawa, ita ce kan gaba wajen zamanantar da yankin, inda wasu kasashen ke kulle jama'arsu, da ma cuzguna musu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng