Yadda aka warewa Fadar Shugaban Kasa makudan kudi a kasafin 2018
- Makon jiya aka aika kasafin kudin badi a gaban Majalisa
- Ana sa rai Najeriya ta kashe sama da Naira Tiriliyan 8
- Fadar Shugaban kasa za ta kashe makudan kudi a ciki
Mun samu labari cewa Fadar Shugaban Kasa ta yi lissafin kashe fiye da Biliyan 1 wajen tafiye-tafiye zuwa Kasashen waje a shekarar 2018.
Idan ba a manta ba a makon jiya Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudin 2018 a gaban Majalisa. Mun gano cewa an warewa Fadar Shugaban Kasa makudan kudi a kasafin kudin na shekara mai zuwa na harkar abinci da sauran abubuwa na rayuwa.
KU KARANTA: Shugaban Kasa Buhari ya isa Kasar Inyamurai
Kamar yadda Jaridar The Cable ta rahoto Shugaban Kasar da Mataimakin sa za su kashe sama da Naira Biliyan daya da miliyan 300 wajen zirga-zirga zuwa Kasar waje. Haka kuma za a kashe sama da Naira Miliyan 20 wajen katin waya a Fadar Shugaban Kasar.
Bayan nan an ware wasu Naira Miliyan 60 da doriya wajen hawa shafin yanar gizo ban da kuma kudin abinci na kusan Naira Miliyan 150 na Shugaban Kasa da Mataimakin sa bayan wasu miliyan 136 na bushasha. Akwai kuma kudin da aka ware wajen sayen fetur.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng