Matsalar Hauwa Kulu ta zo ƙarshe, Sarkin Musulmi ya ɗauki nauyinta – Ini Dr Mansur Sakkwato

Matsalar Hauwa Kulu ta zo ƙarshe, Sarkin Musulmi ya ɗauki nauyinta – Ini Dr Mansur Sakkwato

Wata yarinya mai suna Hauwa Kulu wanda tayi fama da matsanancin ciwo tsawo wata da watanni ta yi gamo da katar bayan da Dakta Mansur ya daura hoton ta tare da bada labarinta a shafinsa na Facebook.

Ita dai wannan yarinya, ta dade tana fama da jinya a kauyensu dake karamar hukumar Isah, kuma shekarunta bakwai a rayuwa, amma saboda tsananin ciwo idan ka ganta ba ka cewa an yaye ta, kamar yadda Masur ya bayyana.

KU KARANTA: Gwamnonin jihohi zasu shirya jarabawar gwaji ga Malaman Makaranta

Majiyar Legit.ng ta ruwaito yarinyar marainiya ce, kuma a hannun kakarta take, ita ma kakar gajiyayya ce, don ko kudin ruwan da za’a kara ma yarinyar basu da shi.

Matsalar Hauwa Kulu ta zo ƙarshe, Sarkin Musulmi ya ɗauki nauyinta – Ini Dr Mansur Sakkwato
Hauwa Kulu

Sai dai cikon ikon Allah, wanda shine mabuwayi gagara misali, mintun 28 da bayyana matsalar Hauwa Kulu da Malam Mansur yayi, sai mai alfarma Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar ya kira shi a waya, kuma ya nemi jin karin bayani akan Kulu.

Bayan zayyana masa duk halin da take ciki, dai Sarkin Musulmi ya dauki alwashin daukar nauyin Hauwa Kulu tun daga yanzu har zuwa samun saukinta, sa’annan ya kara da daukan nauyin karatun ta.

Bugu da kari, Mai Afarma yayi alkawarin tallafa ma gidansu Hauwa da kayan abinci da duk wasu bukatunsu har inda hali yayi, nan take ya hada Mansur da jami’in da zai kula da wannan hidima.

Allah ya kara ma sarki daraja, da tsawon rai mai albarka, kuma Allah ya saka ma duk wanda suka taimakin wannan yarinya da alherinsa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng