Wanene mutumin da ya fi kowa arziki a Tarihi
- Wannan karo za ku ji labarin Attajirin da ba a taba yin irin sa ba
- Sarki Mansa ya mallaki dukiyar da Duniya ba ta taba gani ba
- Musa Mansa ya rayu ne a Garin Timbuktu a can Kasar Mali
Za ku ji labarin Sarki Musa Mansa na Kasar Mali wanda ya mallaki dukiyar da Duniya ba ta taba gani ba a lokacin sa shekarun baya.
Tarihi ya nuna cewa ba a taba samun mutumin da ya mallaki dukiya irin wani Sarki da aka yi a Kasar Timbuktu ta Mali a shekarun 1280 zuwa 1337. Har yau dai babu wanda ya isa ya fada maka iya arzikin Sarki Mansa a Duniya.
KU KARANTA: Ko ka san Jami’a ta farko a Duniya?
Dukiyar Sarki Mansa dai ta wuce Misali don kuwa a lokacin da Musa Mansa ya bar kasar sa zuwa aikin Hajji a Saudiyya ya tsaya Kasar Misra inda ya kashe kudi na rashin hankali har ta kai an shiga rudun tattali a Kasar ta Arewacin Afrika.
Mansa ya samu arzikin sa ne a wajen harkar gwal a lokacin da aka rika neman gwala-gwalai a Duniya. Kasar Mali tayi kaurin suna lokacin da arzikin gwal.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng