Wani matashi dan kabilar Ibo da ya amshi musulunci ya sha yabo (Hotuna)
A kwanakin baya Legit.ng ta kawo muku rahoton wata mace yar kabilar Ibo mai suna Aisha Obi, toh yanzu kuma a jiya Juma'a wani matashi mai suna Chibuzor Yusuf shima ya karbi musluncin kuma ya sha yabo wurin musulman Najeriya a shafin sada zumunta na Facebook bayan ya kyale addinin kirista da yakeyi a baya ya amshi musulunci.
Wani matashi (Igwe Muhammed Sabastine) dan kabilar igbo daga garin Orlu na jihar Imo mai amfani da shafin sada zumuntar facebook din ne ya saka hoton Yusuf tare da yi masa murnar amsar addinin musuluncin.
Sauran al'umma masu amfani da shafin sada zumuntar na facebook sun tofa albarkacin bakinsu akan musuluntar Chibuzor Yusuf din.
Ga dai hotunnan irin sa albarka da al'umma sukayi a kasa.

DUBA WANNAN: Allahu Akbar! Wata mata 'yar Kabilar Ibo ta bayyana soyayyarta ga addinin musulunci



Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng