Malaman Islamiyya sun koka da riƙon sakainar kashi da Iyaye ke yi ma karatun Islamiyya

Malaman Islamiyya sun koka da riƙon sakainar kashi da Iyaye ke yi ma karatun Islamiyya

Malaman Makarantun Islamiyyu sun koka kan yadda iyayen yara ke nuna halin ko in kula ga ilimin addinin Musulunci, ta hanyar rashin sanin muhimmancinsa, inji rahoton BBC Hausa.

Malaman sun bayyana ma majiyar Legit.ng cewar basa samun damar baiwa dalibansu ilimin daya dace sakamakon yawancin su na zuwa Islamiyyah ne a ranakun Asabar da Lahadi na kowanni sati ne kadai.

KU KARANTA: Wani Ɗan-Daudu dake yaudarar samari ya shiga hannu a garin MInna, kalli yadda aka kwashe

Hakan ya sa Malaman suka yi korafi, inda suka ce a wasu lokuttan ma, ko a ranakun Asabar da Lahadin ma daliban basa zuwa Islamiyya, saboda iyayensu kan tafi dasu wajen bukukuwa ko wajen shakatawa.

Malaman Islamiyya sun koka da riƙon sakainar kashi da Iyaye ke yi ma karatun Islamiyya
Daliban Islamiyya

Malaman sun daura laifin akan Iyaye kacokam, saboda a cewarsu yaran sun fi mayar da hankali tare da nuna fifko ga makarantun Boko, banda ilimin addinin Musulunci.

Wata matsala da Malaman suka ce suna fuskanta daga iyayen yara shine rashin biyan kudin makaranta, duk kankantarsa, amma a makarantun Boko ba sai an fada ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel