Wani matashi ya rasa ransa a yayin da fulani makiyaya da manoma su ka cakusa a Nassarawa

Wani matashi ya rasa ransa a yayin da fulani makiyaya da manoma su ka cakusa a Nassarawa

- Sabon rikici ya barke tsakanin fulani makiyaya da manoma a Awe na Jihar Nasarawa

- Rikicin ya barke ne sakamakon makiyayan sun barnata gonar wani mutum

- Matashin ya rasa ran sa ne sakamakon saran shi da makiyayan su ka yi

Hukumar 'yan sanda na Jihar Nasarawa, ta tabbatar da rasuwan Hassan Papalolo, mai shekaru 28. Hassan ya rasa ran sa ne sakamakon sabon rikici da ya balle tsakanin fulani makiyaya da manoma da Karamar Hukumar Awe na Jihar.

Mai magana da yawun Hukumar, DSP Idrisu Kennedy, ya ce Hassan na daya daga cikin wadanda su ka nuna rashin amincewar su game da barnar da makiyayan su ka yi a gonar wani mai suna Yunusa Makeri.

Rikicin makiyaya da manoma: Manomi 1 ya rasa ransa a jihar Nassarawa
Rikicin makiyaya da manoma: Manomi 1 ya rasa ransa a jihar Nassarawa

Nan ne fa makiyayan su ka sare shi da makami, wanda hakan shi ne ajalin sa. A yayin da Makeri da makiyaya guda 2 kuma su ka tsira da munanan raunuka. Matasa sun hana a ba a ba wa makiyayan kula a asibiti, har sai da Sarkin Awe, Alhaji Abubakar Umar, ya rarrashe su

Kennedy ya ce tuni dai a ka aika da jami'an tsaro a yankin domin kwantar da tarzomar.

Alhali kuwa, Kungiyar Fulani ta Miyatti Allah, ta yi kira ga gwamnati tarayya da murya nai karfi, don a kawo masu tallafi kan tsattsauran dokar a ka gindaya ma fulani makiyaya a Jihar Benue.

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164