Duniya ta samu: Dubi hotunan Cristiano Ronaldo cikin katafaren jirgin sa na sama
Yayin da ya samu hutu biyo bayan samun nasarar kasar sa na samun tikitin zuwa kasar Rasha domin kwafsawa a gasar cin kofin Duniya na shekarar 2018, shahararren dan wasan kwallo kafa, Cristiano Ronaldo, ya shilla a cikin jirgin sa domin wata tafiya da ya kira ta kulla wasu harkokin kasuwanci.
Ronaldo ya yi tafiyar ne da tsohon abokin wasan sa lokacin yana kungiyar Sporting Lisbon, Jose Semedo.
DUBA WANNAN: Kwalejin Ado-Ekiti ta ci tarar duk daliban ta N20,000 saboda boren da suka yi
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Jaridar Forbes ta bayyana Ronaldo a matsayin dan wasa mafi arziki na wannan shekarar bayan da ya samu zunzurutun kudi har Yuro miliyan 71 cikin watanni 12. Mafi yawan kudin dan wasan sun zo ne daga talla daga kamfanoni daban-daban duk da kasancewar dan wasan na harkokin kasuwanci, musamman harkokin motsa jiki, turare da otal.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng