Fursunoni mata na karuwa a duniya

Fursunoni mata na karuwa a duniya

Rahotanni sun kawo cewa bincike da aka gudanar ya nuna hauhawan yawan mata dake karuwa a gidan kurkuku a fadin duniya.

Bisa ga binciken yanzu haka akwai mata sama da 700,000 dake zaune a gidan kurkuku a duniya.

Wata matattarar bincike a kan manyan laifuka dake birnin Landan, ta sanar da cewa adadin matan da ke zaman gidan kaso na hauhawa a kowacce yanki a cikin shekaru 17 da suka gabata, kuma an fi samun hauhawan adadin fursunoni mata ne a kasashen Brazil da Indonesia da Phillipines da kuma Turkiya.

Fursunoni mata na karuwa a duniya
Fursunoni mata na karuwa a duniya

Cibiyar binciken ta ce, inda kuma ake da yawan fursunoni mata su ne kasar Amurka da kuma kasar Sin.

KU KARANTA KUMA: Farashin kayayyakin abinci zai ci gaba da sauka – Lai Mohammed

A shekara ta 2015, Sin ta samu karuwar fursunoni mata da yawa wadanda suka aikata laifukan da suka hadar sa sarafar miyagun kwayoyi da kuma cin hanci inji cibiyar.

Hakan ya sa kasar Sin zamowa kasa ta biyu a duniya da ke da yawan fursunoni mata.

Sai dai duk da haka yawan fursunoni mata na kasar Sin bai kai rabin fursunoni matan da ke Amurka ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng