Labarai Cikin Hotuna: Yadda wata matashiyar soja ta tashi hankullan maza a dandalin sada zumunta
Wata matashiyar sojin kasan Najeriya mai sunan Porch Army girl ta sanya mutane da dama musamman maza sun dimaunce yayin da ta yada hotunan ta a dandalin sada zumunta na Instagram.
Wannan matashiya Porch ta shahara da tallace-tallace da ake bukatar mata su yi sanadiyar irin kyawun sura da Mau duka ya zuba mata, wanda hakan ya sanya maza da dama ke yin rububi a kanta ko sa samu damar kulla abota da ita a dandalin na sada zumunta.
Legit.ng ta ruwaito cewa, wannan matashiya ta shahara da yin tallace-tallacen magungunan gargajiya na kamfanin Nigerian herbal Products Company. Ta kuma shahara da yin tallace-tallacen kayan sanyawa a jiki da dinkuna na mata sakamakon nasibi na iya kwarkwasa da kuma lankwashe-lankwashe da take da shi.
KARANTA KUMA: Ma'aikatar Fashola ta samu kaso mafi girma a kasafin kudi
Wannan ba shine karo na farko da labarin matashiyar sojin ya bayyana ba, domin kuwa a yayin da take karkashin soji masu kula da masu yiwa kasa hidima na shekarar 2016 a sansanin su na jihar Legas, ta zamto abar soyuwa a zukatan maza da mata.
LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng