Kungiyar CAN ta bukaci Najeriya ta fita daga Kungiyar musulunci ta OIC

Kungiyar CAN ta bukaci Najeriya ta fita daga Kungiyar musulunci ta OIC

- CAN ta bukaci Najeriya ta fita daga Kungiyar Kasashen Musulunci ta OIC da duk wata Kungiyar Musulunci

- Ta bukaci Majalisar Dokoki ta bayar da takardun hakkin mallaka ga coci-cocin da su ke Arewa

- Ta kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta magance matsalolin da Kasar ke fuskanta

A ranar Talata ne Shuwagabannin addinin kirista su ka yi kira ga Majalisar Dokoki da ta tsaya tsayin daka, don tabbatar da Najeriya ta fita daga Kungiyar Kasashen Musulmai ta OIC da duk wata kungiyar kasashe na musulunci.

Sun yi wannan kira ne yayin wani taro da su ka yi a legas, karkashin jagorancin shugaban CAN, Rabaran Samson Ayokunle. A taron, sun tattauna matsalolin da cocin ke fuskanta da kuma wasu matsalolin da Kasar ke fuskanta.

Kungiyar CAN ta bukaci Najeriya ta fita daga Kungiyar musulunci ta OIC
Kungiyar CAN ta bukaci Najeriya ta fita daga Kungiyar musulunci ta OIC

Adebayo Oladeji, mai magana da yawun shugaban CAN, ya ce Kungiyar ta yi tir da shigar Najeriya cikin kungiyoyin musulunci. Sun kuma bukaci Majalisar Dokoki ta bayar da takardun mallaka ga coci-cocin da su ke Arewa.

DUBA WANNAN: Rufe lambar mota laifi ne - Hukumar FRSC

CAN ta kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da Gwamnatin Jihohi da su magance matsalolin albashi da na rashin aikin yi da kiwon lafiya da dai sauran matsalolin da Kasar ke fuskanta.

Ta kuma yi tir da jami'an tsaro game da gazawar su na magance barnar da fulani makiyaya ke yi. A nan ne ta bukaci a farfado da kungiyar addinai mabambanta. a cewar ta, kungiyar ta taimaka gaya wurin samar da fahimta tsakanin addinin musulunci da na kirista.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

KU LATSA: Sabuwar manhajar labarai na Legit.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164