Wata mata ta haihu ana tsaka da wa’azin ƙasa na Ƙungiyar Izala, ta gamu da sha tara na Arziki
- Mace mai juna biyu ta haihu yayin wa'azin kasa
- Malaman Izala sun taiamaka mata
Rariya ta ruwaito wata mata mai dauke da juna biyu data haihu yayin da ake tsaka wa’azin kasa wanda kungiyar Izala ta shiryawa a ranar Asabar 4 ga watan Nuwamba, a jihar Neja, yankin Arewa ta tsakiya.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito matar wanda ta fito daga kauyen Kwanga na karamar hukumar Ingaski na jihar Kebbi, ta halarci taron wa’azin ne tare da mijinta, inda ta haihu a daidai lokacin da Sheikh Abdullahi Bala Lau ke gabatar da wa’azi, da misalin karfe 11 na dare.
KU KARANTA: Nafisa Abdullahi ta gagara a Kannywood, ta lashe gagarumar kyauta a birnin Landan
Ana cikin wa’zi sai labara ya ishe Shugaban Izala, Sheikh Bala Lau, inda yayi ma yaron addu’a, kuma ya bukaci a sanya ma yaron da aka haifa sunan Malam Abubakar Giro.
Sai dai shima Sheikh Giro Argungu ya shawarci mijin matar daya sanya ma yaron sunan Sheikh Abdullahi Bala Lau, inda uban yaron ya amince, kuma a nan take ya rada masa suna Abdullahi.
Bayan haka sai jama’a da dama suka fara bayar da tallafi ga mahaifiyar yaron, inda wani mutum ya dauki nauyin ragon suna, tare da kyautar dubu goma, kungiyar Izala ta baiwa iyalin naira dubu hamsin, sai kuma Alhaji Sani Basket ya basu buhunan gero, shinkafa, masara da turmin atmfa guda biyu.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng