LABARI DA DUMI-DUMI: Yariman kasar Saudiyya da wasu sun yi hadarin jirgin sama
- Yariman kasar Saudiyya ya yi hadarin jirgin sama tare da wasu jami’an gwamnati
- Hadarin ta auku a yankin Asir kusa da iyakar kasar Yamal
- Yariman da sauran mutanen sun rasa ransu sakamakon hadarin
Yariman kasar Saudi Arabiya da wasu jami'an gwamnati sun mutu a wani mumunar hadarin jirgin sama a Saudiyya a kusa da iyakar Yamal.
Wani rahoto da Al Arabiya ta bayar a ranar Lahadi, 5 ga watan Nuwamba da yamma ta ce jirgin helikafta ya rusha da su a kudu maso yammacin yankin Asir na kasar.
Jaridar ta ce Yarima Mansour bin Muqrin, mataimakin gwamna yankin Asir, ya mutu a cikin hadarin tare da sauran manyan jami'an gwamnati.
KU KARANTA:Ta’addanci: ‘Yan tawayen Houthi sun kai wa Saudiyya hari da makami mai linzami
Idan dai baku manta ba a karshen makon nan ne Legit.ng ta ruwaito cewa hukumar sojin Saudiyya tace ta dakile wani makami mai linzami da ‘yan tawayen Houthi suka harba zuwa filin jirgin sama na King Khalid dake arewa maso gabashin Riyadh.
Ku saurari cikakken bayani daga baya ...
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng