Kotu ta aike da mazaje 2 gidan wakafi bisa zargin su da zina da matan aure

Kotu ta aike da mazaje 2 gidan wakafi bisa zargin su da zina da matan aure

- Kotu ta aike da wasu mazaje 2 mazauna garin Zaria gidan wakafi bisa laifin ajiye matan aure a gidansu da kuma yin zina da ita

- Matar auren dai ta baro gidan mijin ta ne bayan sun sami sabanni misalin karfe 11 na dare inda ta hadu da daya daga cikin mazajen

- Duka mazajen 2 sun yarda cewa matar ta zauna tare dasu har tsawon kwanaki biyar amma sun musanta cewa sunyi zina da ita

Wata babban kotun shari'a da ke zama a Tudun Wada Zaria ta aike da Usman Yusuf da kuma Rabiu Muhammadu zuwa gidan wakafi na makonni 2 bisa laifin ajiye matan aure a gidan su da yin zina da ita har na tsawon kwanaki 5.

A yayin da suke amsa tambayoyin da Alkali ke musu, Rabiu Mohammed ya amince da cewa shine ya kai matar auren gidan abokin sa da ke Layin Nabawa a Tudun Wadan Zaria amma yace baiyi zina da ita ba.

Kotu ta aike da mazaje 2 gidan wakafi bisa zargin su da zina da matan aure
Kotu ta aike da mazaje 2 gidan wakafi bisa zargin su da zina da matan aure

Shi kuwa mutum na biyu da ake tuhuma, wato Usman Yusuf ya amince da cewa matar da zauna gidansa har tsawon kwanaki 5 amma bai san tana da aure ba kuma baiyi zina da ita ba.

DUBA WANNAN: Hukumar INEC tayi kira ga majalisar tarayya tayi gagawar amincewa da kudirin sabin dokokin zabe

Bayan sauraran bayanan su, Alkalin babban Kotun Shari'ar, Aminu Sa'ad ya aike da mazajen 2 gidan wakafi sannan ya bada umurnin a kai matan asibiti domin likitoci su duba lafiyarta.

Matar dai tace sun sami sabani da mijin ta ne shi yasa tabar gida misalin karfe 11 na dare inda ta hadu da Rabiu Mohammed kuma ta bishi zuwa gidansa.

Shi kuwa mijin matan bai ce da manema labarai ufan ba.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164