Asibitin fadar shugaban kasa: Rayuwar Buhari da ta iyalansa na cikin hatsari – Majalisar wakilai

Asibitin fadar shugaban kasa: Rayuwar Buhari da ta iyalansa na cikin hatsari – Majalisar wakilai

- Majalisar wakilan Najeriya tace bazata bari rayuwar shugaban kasa Buhari ya kasance cikin hatsari ba

- Majalisar ta fadi hakan ne yayin martini ga tabarbarewan asibitin fadar shugaban kasa da kuma rashin shugabanci mai kyau a tare da ma’aikatan asibitin

- Sun kuma yi Allah wadai da rashin kayayyaki masu daga gwamnatin baya

Kwamiti da majalisan wakilai ta nada kan binciken Asibitin Aso Rock ta bayyana cewa baza ta yarda rayuwan shugaba Muhammadu Buhari da iyalensa baza su kasance cikin hatsari ba ganin yanda asibitin ta tabarbare.

Kwamitin, wanda Hon. Magaji Aliyu ke shugabanta, ya ce akwai bukatan ingantaccen kayan kula da lafiya ko da an samu al’amari dake bukatar kulawa cikin gaggawa.

Asibitin fadar shugaban kasa: Rayuwar Buhari da ta iyalansa na cikin hatsari – Majalisar wakilai
Asibitin fadar shugaban kasa: Rayuwar Buhari da ta iyalansa na cikin hatsari – Majalisar wakilai

Magaji ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da Ismaila Kawu, mai magana da yawun shugaban kasa kan harkokin majalisan dattawa; Ita Enang, mai magana da yawun shugaban kasa kan majalisan wakilai; Osagie, Enahire, ministan lafiya da kuma mai wakilcin Muhammad Bello, ministan tarayya, a harabar majalisan dokoki, a Abuja.

Shugaban kwamitin tare da wassu yan majalisan sun bayyan damuwarsu bisa ga jawabai da ministocin suka gabatar a baya, wanda suke ikirarin cewa basu sane da halin da asibitin fadar shugaban kasa take ciki, sun nuna bacin rai kan yanda gwamnatoci da suka gabata suka nuna rashin kulawa da kayan aiki da kuma yanda ake gudanar da ayyuka a asibitin.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng