Goron Juma’a: Mutanen da Allah ba ya kauna a Duniya

Goron Juma’a: Mutanen da Allah ba ya kauna a Duniya

- Mun kawo Mutane 4 da Allah ba ya kauna a Duniya

- Daga ciki akwai tsohon da ya tsufa ba ya gudun zina

- Akwai kuma Matalaucin mutum mai mugun girman kai

A Rana irin ta yau mun kawo maku wani Hadisi na Manzon Allah Annabi Muhammadu SAW inda ya bayyana wasu mutane 4 da Ubangiji Madaukaki ba ya kaunar su a Duniya saboda mugun halin su. Wadannan mutane dai su ne:

1. Matalauci mai girman kai

Kamar yadda Marigayi Malam Ja’afar Mahmud Adam ya bayyana daga cikin wadannan mutane akwai wanda ke fama da mugun talauci amma kuma yake da dan-karen girman kai.

KU KARANTA: An hana wani Malamin addini wa'azi a Zambia

2. ‘Dan kasuwa mai yawan rantsuwa

Haka nan kuma akwai ‘dan kasuwar da yake yawan rantsuwa bini-bini a duk lokacin da zai saida kaya a kasuwa. Musamman kuma ace mutum karya yake yi wajen ratsuwar.

3. Dattijo mai yawan zina

Akwai kuma tsohon da ba ya gudun zina duk da shekarun sa sun yi nisa amma ba ya jin tsoron Allah. Ubangiji Madaukaki SWT ba ya son irin wannan mutumi.

4. Azzalumin mai mulki

Na karshen su dai a Hadisin shi ne kuma wanda ya samu mulki amma kuma yake kuma kuntatawa Jama’ar sa na Talakawa da damar da ya samu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng