Bamu daukan sabin ma'aikata a halin yanzu - Hukumar FAAN
- Hukumar Tashoshin Jirgin Sama ta yi magana game da daukan ma'aikata
- Ta ce 'yan damafara ne ke ikirarin su na daukan aiki a madadin Hukumar
- Don haka ta fito ta nesanta kanta da ga irin wadannan 'yan damfara
A ranar Alhamis ne Hukumar Tashoshin Jirgin Sama na Najeriya (FAAN), ta fito ta nesanta kanta da wata kamfanin 'yan damfara da ke damfaran mutane ta hanyar fakewa da daukan aiki a madadin FAAN.
Hukumar ta gargadi 'yan Najeriya da su yi taka tsan-tsan da irin wadannan kamfanoni. Ta kuma yi matashiya kan yadda daukan aiki a gwamnatance ya ke da tsari, wanda a fari, a na tallatawa ne a manyan jaridu.
Don haka ta yi kira ga jama'a da su kai karan duk wanda ya zo masu a matsayin jami'i mai daukan aiki na Hukumar.
DUBA WANNAN: Dokar Hana Yawon Kiwo: A na zargin Fulani Makiyaya da kashe wani mutum
Wannan gargadi ya fito ne daga bakin Janar Manaja na harkokin hulda na Hukumar, mai suna Misis Herrienta Yakubu.
Hukumar ta jaddada cewan za ta ci gaba da sauke nauyin ta na ankarar da jama'a game da irin wadannan miyagun mutane don tabbatar da tsaro da walwalar al'umma.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng