Iyalan marigayi Kanal Abu Ali zasuyi masa addu’an shekara daya
- Iyalan marigayi Kanal Abu Ali zasuyi masa addu’an shekara daya
- Kanal Abu Ali ya kasance jarumin soja da ya sadaukar da ransa wajen yaki da ta'addanci a ksar
- Ya rasu a ranar 4 ga watan Nuwamban 2016 a garin Mallam Fatori dake jihar Borno
Ahlin gidan marigayi Laftanal Kanal Abu Ali, wani jarumin soja da yayi ma kasa idima wajen yakar Boko Haram, sun shirya gudanar da addu’an shekara daya domin tunawa da marigayin dansu yayi da ya cika shekara daya da rasuwa.
Rundunar soji ta aika marigayi Laftanal Kanal Muhammad Abu Ali yankin Arewa maso gabashin Najeriya domin ya yaki yan ta’addan Boko Haram sannan kuma yayi yaki iya karfinsa domin dawo da martabar kasar sa yayinda ya rasa ransa domin ganin ya dawo da farin ciki da zaman lafiya a kasar Najeriya.
KU KARANTA KUMA: 2019: Atiku ya kaddamar da kudirinsa na tsayawa takarar shugabancin kasa
A wata sanarwa dauke da sa hannun mahaifin marigayin, Etsu Bassa Nge, Birgediya Janar Abu Ali (mai ritaya) yace dansu ya yi jihdi mai tsada ta hanyar fuskantar Boko Haram a filin daga tsakanin rundunar soji da yan ta’adda a garin Mallam Fatori, Arewacin jihar Borno da misalin karfe 10:00 na daren ranar Juma’a 4 ga watan Nuwamban 2016.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng