Maina: Shugaba Buhari ya gana da Abdurrahman Dambazau
- Shugaba Buhari yayi wani zama na musamman da Dambazzau
- Hakan na zuwa ne bayan Shugaban ya gana da su Abba Kyari
- Maganar ba ta wuce ta Abdurrasheed Maina na kwamitin fansho
Mun fahimci cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gana da daya daga cikin Ministocin da ake zargi da dawo da Abdurasheed Maina ofis.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a jiya kamar yadda majiyar mu ta bayyana mana ya gana da Ministan harkokin cikin gida Janar Abdulrahman Dambazau (retd) wanda yana cikin wadanda ake zargi da yin kutun-kutun wajen dawo da Maina aiki.
KU KARANTA: Ka manta da mu Baba Inji wasu 'Yan APC ga Buhari
Ganawar Shugaban kasar ta biyo bayan zaman da Shugaba Buhari yayi ne da Shugaban Ma’aikatan fadar sa Abba Kyari da kuma Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya Winfried Oyo-Ita bayan takaddamar da ya kaure a Fadar Shugaban kasa shekaran jiya.
Ana dai ta ce-ce-ku-ce a Kasar game da batun Abdurrasheed Maina wanda da fari Gwamnatin Buhari ta dawo da shi aiki ta bayan fage duk da irin zargin da ke kan sa. Wasu dai na zargin cewa Shugaban kasar ya san duk abin da ya faru da farko kafin ya sa a sallame sa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng