Za’a yi janai’izar matar sanata Goje, Hajiya Fatima Yelwa a gobe Juma’a
Rahotanni sun kawo cewa za’ayi jana’izar uwargidan tsohon gwamnan jihar Gombe, sanata Danjuma Goje, marigayiya Hajiya Fatima Yelwa a ranar Juma’a, 3 ga watan Nuwamba.
Za’ayi jana’izar ne a kofar gidan mai martaba sarkin Gombe da misalin karfe 2:00 na rana wato bayan sallar Juma’a.
A baya Legit.ng ta rahoto cewa Hajiya Yelwa Danjuma Goje, matar tsohon gwamnan jihar Gombe, Sanata Mohammed Danjuma Goje, ta rasu a wani asibiti dake kasar Amurka.
KU KARANTA KUMA: Muna rasa magoya baya a kullun – Kungiyar Buhari
Ahmed Mohammed Goje, dan tsohon gwamnan ya sanar da mutuwar mahaifiyarsa a ranar Litinin, 30 ga watan Oktoba, a wata sanarwa da ya fitar a madadin ahlin gidan.
Sanarwan ya kasance kamar haka: "Tare da godiya ga Allah madaukakin sarki, Ina bakin cikin sanar da rasuwar mai girma, Hajiya Yelwa Danjuma Goje, matar tsohon gwamnan jihar Gombe, Sanata Mohammed Danjuma Goje."
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng