Wata yarinya mai kambun baka tayi ma ƙawarta baki, ta makance gaba daya
Ta tabbata kambun baka abu ne tabbatacce, wanda ko a tarihi an samu labaransa, hakan ta sa manzon tsira Annabi Muhammadu (S.A.W) ya ja hankalin mutane akan furta magana yadda suka ga dama.
A jihar Kano an samu wata yarinya mai suna Khadija, wanda a yanzu haka ta makance murus, tun bayan da wata kawarta da ake zargin tana dauke da kambun baka tayi mata mummunan fata.
KU KARANTA: Rundunar Yansandan jihar Filato tayi nasarar tarwatsa wasu gungun yan fashi da makami
Ita dai Khadija ta bayyana cewar tana zaman zamanta, sai kawarta tace mata, zata ta mutu, ko kuma ta makance, kwatsam kuwa sai ga makanta ya samu Khadija, wanda a kimanin kwanaki goma sha daya kenan bata gani gaba daya.
Wani ma’bocin kafar sadarwar Facebook, Bashir El-bash ne ya bayyana wannan labara mai cike da tausayi, inda yace tuni hukumar kare hakkin bil adama, mai suna Human Right Network of Nigeria ta shiga maganan.
Majiyar Legit.ng yace a yanzu dai an garzaya gaban kuliya manta sabo, don tabbatar da an kwato ma Khadija hakkinta, inda yace za’a cigaba da sauraron karar a Kotu gidan Murtala a ranar Alhamis 2 ga watan Nuwamba.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Kalli yadda aka karrama Legit.ng TV
Asali: Legit.ng