Sai Buhari ya bar mulki za mu tona asirin Gwamnatin sa – Tukur Mamu
- Tukur Mamu yayi kaca-kaca da Gwamnatin Shugaba Buhari
- Mamu yace Shugaba Buhari ba da gaske yake yaki da barna ba
- ‘Dan jaridar yace sai lokacin zabe ne Jama’a za su san gaskiya
Mun samu labari cewa Babban ‘Dan jaridar nan Alhaji Tukur Mamu yayi kaca-kaca da Gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a wata hira da mu ka samu a makon nan inda yace akwai munafunci a yaki da rashin gaskiyar wannan Gwamnati.
Tukur Mamu mai Jaridar Desert Herald yace sai lokacin zabe Jama’a za su san gaskiyar lamarin inda yace bayan Shugaba Buhari ya bar mulki, za a fahimci irin zaluncin da aka tafka a karkashin Gwamnatin sa wanda yace gara ma lokacin mulkin PDP.
KU KARANTA: Buhari ya fadawa EFCC su yi ram da Babachir David Lawal
Mamu wanda a da ya goyi bayan Buhari ya nuna irin son kan da ke cikin yaki da rashin gaskiya a Gwamnatin nan inda yace akwai wadanda ake gudun tabawa don haka ne ma da fari aka gaza yi wa tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya Babachir Lawal komai.
A cewar sa ma dai Shugaban kasar ya san duk abin da ya faru game da batun Abdurrasheed Maina amma yayi murus har sai lokacin da abubuwa su ka cabe. Mamu yace Gwamnatin Buhari ta rainawa ‘Yan Najeriya hankali matuka.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng