Allahu Akbar! Wata mata 'yar Kabilar Ibo ta bayyana soyayyarta ga addinin musulunci

Allahu Akbar! Wata mata 'yar Kabilar Ibo ta bayyana soyayyarta ga addinin musulunci

- Matar mai suna Aishat Obi, ta yi ridda ne daga addinin kirista

- Ta yi kira ga musulmai da su ware lokaci don koyon addinin

- Ta kuma kira ga sauran musulmai 'yan kabilar Ibo da su kasance masu juriya

Wata mata 'yar Kabilar Ibo, mai suna Aishat Obi, ta bayyana soyayyar ta ga musulunci bayan ta yi ridda daga addinin kirista. A cewar ta, ta na alfaharin kasancewar ta musulma duk da kalubalen da hakan zai iya haifar wa.

A bayanin da ta yi a shafin ta na Facebook, ta yi kira ga musulmai da su samar wa kan su lokacin koyon addini domin kuwa ta ce musulunci ba a fatar baki bane. .

Allahu Akbar: Wata 'yar kabilar ibo da ta karbi musulunci ta bayyana farin cikin ta
Allahu Akbar: Wata 'yar kabilar ibo da ta karbi musulunci ta bayyana farin cikin ta

Ta kuma jawo hankalin sauran musulmai 'yan kabilar ta Ibo, da su yi hakuri su jurewa matsi da zagi da za su fuskanta sakamakon musuluncin na su. Ta ce musulunci kuwa a kasar Ibo, nan gani nan bari.

Allahu Akbar: Wata 'yar kabilar ibo da ta karbi musulunci ta bayyana farin cikin ta
Allahu Akbar: Wata 'yar kabilar ibo da ta karbi musulunci ta bayyana farin cikin ta

Ta kuma shawarci sauran musulman da su bi hanyar da ta dace don kai karar duk wanda ya yi barazanar cutar da su.

DUBA WANNAN: Yanzu Yanzu: Dasuki ya bayyana a kotu don shari'ar Metuh

Allahu Akbar: Wata 'yar kabilar ibo da ta karbi musulunci ta bayyana farin cikin ta
Allahu Akbar: Wata 'yar kabilar ibo da ta karbi musulunci ta bayyana farin cikin ta

Ta kuma ce ga duk me neman shawara kan hanyar da zai bi don magance wata barazana, to ya tuntube ta da rubutaccen sako a shafin nata na Facebook

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164