Gubar abinci da wata mata ta shiryawa angon ta ta kashe surukan ta 15 a kasar Pakistan
Wata amarya mai shekaru 21 da aka yi mata auren dole a kasar Pakistan ta shiga hannun jami'an tsaro sakamakon kisan surukan ta 15 a kokarin ta na kisan mai gidan na ta bayan ta sanya mi shi guba a abinci.
Wannan mata Aasia Bibi ta gudu gidan iyayenta bayan watanni biyu kacal da aure, inda suka tursasa ta ta koma dakin mijin ta.
A fahimtar Legit.ng da sanadin jaridar Daily Post ta ruwaito cewa, tsohon masoyin wannan amarya Shahid Lashari, shi ya ba ta guba domin ta zubawa mijin ta a cikin abinci kowa ya huta.
Hausawa na cewa tsautsayi ba ya wuce ranar sa, domin kuwa a maimakon mijin ya yi amfani da wannan abin sha da ta hada masa, sai kwatsam surukan ta suka yi amfani da shi ta hanyar hada wani abin sha na daban mai sunan Lassi na gargajiya irin ta su.
KARANTA KUMA: Fataucin hodar shaidan ya jefa wata mata shekaru 10 a gidan kaso
A yayin haka ne surukan Bibi 27 suka kwankwadi wannan abin sha, wanda cikin kankanin lokaci idanuwa suka fara raina fata domin kuwa nan take mutum suka sheka lahira sauran mutum 12 kuma suna nan cikin jiran tsammanin yau ne ko gobe.
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng