Allah yayi wa matar Sanata Danjuma Goje rasuwa
Hajiya Yelwa Danjuma Goje, matar tsohon gwamnan jihar Gombe, Sanata Mohammed Danjuma Goje, ta rasu a wani asibiti dake kasar Amurka.
Ahmed Mohammed Goje, dan tsohon gwamnan ya sanar da mutuwar mahaifiyarsa a ranar Litinin, 30 ga watan Oktoba, a wata sanarwa da ya fitar a madadin ahlin gidan.
Sanarwan ya kasance kamar haka: Tare da godiya ga Allah madaukakin sarki, Ina bakin cikin sanar da rasuwar mai girma, Hajiya Yelwa Danjuma Goje, maar tsohon gwamnan jihar Gombe, Sanata Mohammed Danjuma Goje.
KU KARANTA KUMA: Mutane biyar sun mutu a wani harin kunar bakin wake da aka kai masallacin Maiduguri
“Tana da shekaru 55, ta rasu a wani asibitin Amurka. Ta mutu ta bar mijinta, Sanata Goje, yara shidda, jikoki 10, da yan uwa da dama.
“Za’a sanar da rana da kuma lokacin jana’iza a Gombe daga baya.”
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng