Allah ya yiwa matar da ta haifi ‘yan hudu a jihar Katsina rasuwa (hoto)
- Wata mata mai shekaru 38 wacce ta haifi yan hudu ta rasu bayan yan kwanaki da haihuwar ta
- Marigayiyan ta haifi yaran ne ta hanayar aiki da akayi mata
- Ance mutuwar matar baya da alaka da aikin da akayi mata
Allah ya yiwa matar da ta haifi ‘yan hudu a babban asibitin Malumfashi dake jihar Katsina rasuwa.
Matar wacce aka ambata da suna Gaje Zubairu ta rasu a jiya Lahadi, 29ga watan Oktoba kwanaki hudu bayan an yi mata aikin fiddo yaran.
Babban Daraktan asibitin, Dakta Abdulhamid Abdullahi ya bayyanawa manema labarai cewa Gaje ta amsa kiran mahaliccinta ne da misalin karfe 11:00 na safe bayan daya daga jariran da ta haifa ya mutu kwanaki biyu bayan haihuwarsu.
KU KARANTA KUMA: Manyan barayi na a jam’iyyar APC – Sule Lamido
An kuma rahoto cewa mutuwar matar baya da alaka da aikin da akayi mata.
Tun bayan haihuwar yaran dai jama’a da dama suka yi ta ziyartar asibitin domin ganin yaran da kuma mika tallafi.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng