Yan fashi sun kashe jigon PDP, da wasu 4 a Zamfara
A ranar Juma’a wasu da ake zargin yan fashi ne sun kai hari sannan sun kashe wasu mutane biyar ciki harsa wani jigon PDP a jihar Zamfara, Alhaji Abdulhadi Saidu Garkuwan Yan ware.
An kuma kawo cewa yan fashin sun rufe wani hanya a tsakanun Funtua zuwa Gusau inda suke ta harbin ababen hawa dake zuwa daga nesa. Sun tsayar sannan suka kashe mutanen dake cikin motan kafin su wargazar dasu da kayayyakin su.
Wani mazaunin garin Alhaji Saidu Maishanu Gusau ya fada ma jaridar Daily Trust cewa an harbi jigon na PDP ne a wuya bayan motar su ta daki hanyar da mayakan suka toshe. Sun bude ma ayarin motocin jigon na PDP wuta.
“Suna a hanyarsu ta dawowa daga jihar Kaduna inda sukayi wani ganawa basu san cewa yan bindigan na fashi a hanyar ba. Direban motan ya rayu amma dai yana karkashin kulawar likita a karamar hukumar Tsafe dake jihar,” inji shi.
KU KARANTA KUMA: Buhari ya ba Saraki da Dogara hakuri kan al’amarin tsaro a Aso Rock
Marigayi Alhaji Abdulhadi Saidu wanda ya rasu yana da shekaru 38 ya kammala karatu ne daga jamiár Usman Danfodio, Sokoto sannan kuma ya kasance jigo a siyasar PDP na jihar.
Ya rasu ya bar matar aure daya da yaro guda sannan kuma ya fito daga karamar hukumar Tsafe na jihar.
Ba’a samu isa ga kakakin yan sandan jihar ba a daidai lokacin wannan rahoto.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng