Jiga jigan fina finan Hausa na da dana yanzu sun taya Fati Muhammad murnan samun babban muƙami a gidauniyar Atiku Abubakar

Jiga jigan fina finan Hausa na da dana yanzu sun taya Fati Muhammad murnan samun babban muƙami a gidauniyar Atiku Abubakar

- Yan Fim sun taya Fati Muhammad murnar samun cigaba a wajen aikinta

- Tsofaffin jarumai da dama sun samu halartar bikin karramawar

Da dama daga cikin tsofaffin jaruman Kannywood, wanda tauraron yake haskawa, da wadanda suka sha miya sun fitar farin dango wajen taya abokiyar aikinsu, Fati Mohammad murnar cigaba data samu.

Iya dai Fati dama tana rike da mukamin darakta mai kula da al’amuran da suka shafi mata a gidauniyar tallafa ma jama’a na tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar mai suna ‘Atiku Care Foundation.’ Kamar yadda Rariya ta ruwaito.

KU KARANTA: Sai mun yi takatsantsan wajen ciyo ma jihar Kaduna bashi – Inji Sanata Shehu Sani

Jiga jigan fina finan Hausa na da dana yanzu sun taya Fati Muhammad murnan samun babban muƙami a gidauniyar Atiku Abubakar
Bikin

Sai dai yan kwanakin da suka gabata ne aka yi mata karin girma sakamakon jajricewarta masu gidauniyar suka tabbatar, inda aka nada ta Daraktar mata ta gidauniyar sashin Arewa maso yammacin kasar nan.

Jiga jigan fina finan Hausa na da dana yanzu sun taya Fati Muhammad murnan samun babban muƙami a gidauniyar Atiku Abubakar
Fati Muhammad

Hakan ya snaya Fati shirya wani kasaitaccen Walima a dakin taro na Aso Motel dake garin Kaduna, taron ya samu halartar tsofaffin yan Fim kamar su Sadiya Gyale, Wasila Ismail, Hadiza Kabara, Hajiya Binta Kofar Soro, Fati Yola, Abida Muhammad, Hauwa Waraka, Fati KK, Rahma Sirace, Fati Washa, Sakna Gadaz, da sauransu.

Jiga jigan fina finan Hausa na da dana yanzu sun taya Fati Muhammad murnan samun babban muƙami a gidauniyar Atiku Abubakar
Jarumai

Daga bangaren maza majiyar Legit.ng ta ruwaito daga cikin jaruman da suka samu halartar wannan taro akwai, shugaban hukumar tace finafinai Hausa Isma'il Na'Abba Afakallah, Rabi'u Rikadawa, Tahir I. Tahir, Adam A. Zango, Jamilu Adamu Kocila, Abbas Sadik, Nasir Koki, , da sauransu da dama.

Jiga jigan fina finan Hausa na da dana yanzu sun taya Fati Muhammad murnan samun babban muƙami a gidauniyar Atiku Abubakar
Jarumai

Jiga jigan fina finan Hausa na da dana yanzu sun taya Fati Muhammad murnan samun babban muƙami a gidauniyar Atiku Abubakar
Jarumai

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng