Boko Haram: Majalisar Dunkin Duniya ba ta yarda da Gwamnatin Buhari ba

Boko Haram: Majalisar Dunkin Duniya ba ta yarda da Gwamnatin Buhari ba

- Majalisar Dinkin Duniya tayi magana game da Boko Haram

- A cewar UN akwai Garuruwan da ke hannun ‘Yan ta’adda

- Shugaba Buhari yayi ikirarin murkushe ‘Yan Boko Haram

Mun samu labari cewa Majalisar Dinkin Duniya tace har yanzu akwai Garuruwan da ke hannun Boko Haram a Jihar Borno.

Boko Haram: Majalisar Dunkin Duniya ba ta yarda da Gwamnatin Buhari ba
Gwamnatin Buhari tace ta gama da Boko Haram

Majalisar Dinkin Duniya watau UN tace akwai Garuruwa 3 da ke hannun ‘Yan ta’adda a Jihar Borno da ke Arewa maso gabashin Kasar. Majalisar ta maidawa Rundunar Sojin kasar raddi ne na cewa babu Garin da ke hannun ‘Yan ta’addan Boko Haram.

KU KARANTA: 'Yan Sanda za su ladabtar da Jami'an ta

A baya Shugaban Kasar Muhammadu Buhari yayi ikirarin Gwamnatin sa ta murkushe ‘Yan Boko Haram daga Yankin. Majalisar tace dai ba haka abin yake ba don watakila ma ‘Yan ta’adda su cigaba da kai wasu hare-haren bayan daukewar damina.

A jawabin da Majalisar akwai Garuruwan da Hukuma ba ta iya kai agaji saboda rashin tsaro. Majalisar ta UN tace iyaka cikin Gari ne kurum Hukumomin agaji ke iya ratsawa a Maiduguri.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng