Aljannu ne su ka aike ni da kudin, in ji wani da 'yan sanda su ka kama da jabun dalar Amurka
- 'Yan sandan Jihar Neja sun yi ram da wani mai suna Abubakar Suleiman, dauke da jabun 880,000 na dalar Amurka
- Suleiman ya ce shi dai dan aiken aljannu ne, bai san kudin jabu bane
- Hukumar 'yan sanda ta ce Suleiman na cikin kungiya masu yawo da kudin bogi wanda ta ke nema ruwa a jallo
Abigail Unaeze, mai magana da yawun Hukumar 'yan sandan Jihar Neja, ta ce 'yan sanda sun yi ciki da wani Abubakar Suleiman yayin da ya kai wa wani Injiniya Abdullahi Sambo jabun 880,000 na dalar Amurka, a yankin Shango na garin Minna.
Wani dan uwan Sambo mai suna Mamman Manya ne ya kai Suleiman kara ofishin 'yan sanda da ke Chanchaga. Suleiman dai ya amsa laifin mallakar jabun kudi amma ya yi ikirarin aljannu ne su ka umurce shi ya karbi kudin a hannun wani mai suna Khalifa.
Suleiman dai ya ce aljannun sun kira shi ne su ka umurce shi ya karbi sako daga hannun Khalifa, ya kai wa Sambo. Ya ce kuma sun yi alkawarin zasu taimake shi da kudi, amma baya ga wanann bayani, bai san komai ba.
DUBA WANNAN: Majalisar Dattawa tana tuhumar Ma'aikatun Gwamnatin Tarayya guda 24 da bannatar da naira biliyan 630
Suleiman ya kuma ce ya yi ta kiran khalifa ta wayar tarho amma ya ki ya daga wayar ta sa. Ita kuwa Hukumar 'yan sanda ta ce, Suleiman ya na cikin wata kungiyar masu yawo da kudaden boge ne wanda daman Hukumar ke neman su ruwa a jallo.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng