Gasar Kwallon kafa: Cristiano Ronaldo ne yafi kowa iyawa a duniya
Labaran da muka samu dai na tabbatar mana da cewa fitaccen dan wasan kwallon kafar nan na kungiyar Real Madrid dake a kasar Sifen watau Cristiano Ronald ne ya lashe gasar dan kwallon duniya a karo na biyar.
Mun samu dai cewa dan wasan ya doke manyan abikan hamayyar sa irin su Lionel Messi dake wasa a kungiyar Barcelona da kuma Neymar dan kasar Brazil da kuma ke buga wasan sa a kungiyar PSG ta kasar Faransa.
KU KARANTA: Zaben 29019: Mutane miliyan 80 ne za suyi hisabi
Legit.ng dai ta samu cewa wannan ne karo biyu da hukumar ta gudanar da nata bikin na karrama fitattun 'yan kwallon duniya bayan rabewar su da mujallar nan ta kasar Faransa dake bayarwa a shekarun baya mai suna Ballon d'Or.
Sauran wadanda suka lashe kyaututtuka a gasar sun hada da Olivier Giroud da ya ci kwallo mafi kayatarwa wato Fifa Puskas, koci namiji da ya fi yin fice shine Zinedine Zidane na kungiyar ta Real Madrid sai kuma mai tsaron raga da babu kamarsa wanda Gianluigi Buffon ya lashe da dai sauran su.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng