Auren Diyar Saraki da wani Kirista ya kawo ce-ce-ku-ce

Auren Diyar Saraki da wani Kirista ya kawo ce-ce-ku-ce

- Diyar Bukola Saraki za ta auri Kirista mako mai zuwa

- Wasu sun soki lamarin inda su kace ya sabawa Addini

- Bukola Saraki Musulmi ne amma matar sa Kirista ce

Labari ya zo mana cewa Babbar Diyar Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Bukola Saraki za tayi aure a karshen makon nan.

Auren Diyar Saraki da wani Kirista ya kawo ce-ce-ku-ce
Tosin Saraki za ta auri Kirista a Legas

Sai dai Tosin Saraki za ta auri wani Kirista ne duk da Mahaifin ta Abubakar Bukola Saraki yana Musulmi. Tosin Saraki za ta auri Saurayin ta ne Adeniyi Olatunde Olukoya wanda ‘da yake wurin Omooba Tokunbo Olusanya.

KU KARANTA: 'Yan wasan yanzu sun fi na da gogewa Inji Umma Shehu

Wasu dai su na ganin wannan aure ya sabawa addinin Musulunci dalili kuwa cewa Addini bai yarda Musulma ta auri wanda ba Musulmi ba. Sai dai Uwargidar Bukola Saraki kuma Mahaifiyar Yarinyar watau Toyin Saraki Kirista ce.

Yarinyar dai tayi karatu ne a Ingila inda yanzu ta ke aiki da babban Kamfanin nan na Uniliver. Za a daura auren ne a Ranar 28 ga Watan nan a Garin Legas. A cewar wasu hakan zai dishe Tauraruwar siyasar Saraki musamman a wajen Musulmai.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng