Miyan Ayoyo ya hallaka Uba, Matarsa, Ýaýansu guda 3 da karensu a jihar Kaduna

Miyan Ayoyo ya hallaka Uba, Matarsa, Ýaýansu guda 3 da karensu a jihar Kaduna

Jama’a a kauyen Dushai dake karamar hukumar Kaura sun shiga cikin dimuwa tare da rikicewa bayan da miyan Ayoyo tayi ajalin wasu iyalai su biyar tare da karensu a kauyen, kamar yadda jaridar Sun ta ruwaito.

Wannan lamari mai muni ya faru ne a ranar Asabar 9 ga watan Satumba, inda Maigidan, wanda tsohon Dansandan Najeriya ne, Peter Dauda ya cika tare dda Matarsa Dorothy mai dauke da juna biyu, dansu Godwin mai shekaru tara, Yarsu Patience da kuma karensu.

KU KARANTA: EFCC ta ƙaddamar da sabuwar farautar Abdulrasheed Maina

Shugaban kauyen Daushi, Daniel Duniya ya bada labarin yadda lamarin ya auku, “Mutanen sun dafa miyan Ayoyo ne a daren Laraba 6 ga watan Satumba, inda suka shanya sauran da nufin maimatawa washegari, daga nan suka kwanta bayan cin abincin.

Miyan Ayoyo ya hallaka Uba, Matarsa, Ýaýansu guda 3 da karensu a jihar Kaduna
Dauda

“Amma a ranar ALhamis, bayan sun maimaita miyan , sai suka fara jin ciwon ciki, inda aka garzaya dasu zuwa Asibiti domin samun kulawa, amma yarsu Patience ce ta fara rasuwa a ranar Juma’a, yayin da Dorothy, Godwin da Dauda suka mutu a ranar Asabar. wannan yasa muke zargin an barbada ma ganyen guba ne”

Daniel Duniya ya bayyana Dauda a matsayin mutumi mai hakuri da sanin dattaku, kuma ya bada gudunmuea mara misaltuwa ga cigaban al’ummar Dushai, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

Shima mataimakin gwamnan jihar Kaduna, Barnabas Bala Bantex ya kai ziyarar ta’aziyya ga jama’an kauyen, inda yace “Ina roko daku manta da duk wasu jita jitan kashe mutanen nan, saboda hakan ka iya kawo tashin tashina a jihar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: