Dan sintiri ya harbe kan shi har lahira domin gwajin laya

Dan sintiri ya harbe kan shi har lahira domin gwajin laya

- Har yanzu dai Hausawa basu bar al'adar layu ba

- Garin gwajin layar bindinga dan sintiri ya harbe kan shi

- 'Yan sanda na nan na bincike

Wani dan sintirin Isan Gona mai suna Ahmadu Maikare ya harbe kan shi har lahira a yayin da yake gwajin sabuwar layar hana harsashi huda mutum. Wannan ya faru ne a kauyen Dubul, da ke karamar hukumar Matazu, a jihar Katsina.

Dan sintiri ya harbe kan shi har lahira domin gwajin laya
'Yan sintirin Isan Gona Hoto: Daily Trust

Mai magana da yawun bakin 'yan sandan Katsina, DSP Gambo Isah, ne ya baiyana wa manema labarai wannan al'amarin. Ya ce har yanzu ana nan ana bincike.

Hakan ya auku ne a yayin da 'yan sintirin suka taru a gidan shugaban su, Sama'ila Rabi'u, domin bikin karrama sabbabin wadanda aka diba aiki a cikin su.

DUBA WANNAN: Sojojin saman Najeriya sun yi wa sansanin 'yan Boko Haram ruwan wuta

Maikare ya tashi tsakiyar jama'a yana tallata layun. Ya daura su a jikin sa yana sunbatun 'yan bori, kana ya dau bindiga yar harbi kan shi. Nan take dalma ta kai shi lahira.

Nan take duk 'yan taron suka arce, sai 'yan uwan sa ne suka zo suka dauki gawar.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, a tuntube mu a:

labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng