Dubi hotunan wata budurwa 'yar kwalisa da 'yan fashi suka yiwa wal-mukalifatu
Jaridar Legit.ng taci karo da wasu hotunan wata kyakykyawar mata da 'yan fashi suka sabawa kamanni a hanyarta ta zuwa wurin aiki a jihar Legas.
Matar mai suna Stella David ta yada hotunan nata da kanta a dandalin sada zumuntar zamani na yanar gizo, tana mai bayyana cewar ta godewa ALLAH data tsira da rai.
Wannan iftila'i ya fada kan wannan baiwar ALLAH ne bayan data hau wata mota zuwa wurin aiki daga Berger amma sai da gangan motar ta bi ta Victoria Island inda 'yan fashin suka far ma ta.
DUBA WANNAN: Gwamnatin tarayya ta bayyana dalilin bawa mai laifin cin hanci mukami a sirrance
Stella ta bayyana cewar 'yan fashin sun kwace mata duk kayayyakin ta, sannan tayi kira da jama'a su kara lura wajen yin amfani da fasahar banki a wayoyin hannu da kuma kula da abun hawa yayin bulaguro.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng