Jihohi 4 ne kawai ke iya biyan albashi ba tare da sun ciyo bashi ba a Najeriya - Kungiyar BudgIT

Jihohi 4 ne kawai ke iya biyan albashi ba tare da sun ciyo bashi ba a Najeriya - Kungiyar BudgIT

- Wata kungiya Inganta zamantakewan al'umma ta fitar da wani rahoto akan yanayin kudaden shiga da jihohin Najeriya ke tara wa

- Sakamakon binciken ya nuna cewa jihohi 4 ne kawai ke da ingantatun hanyoyin samun kudin shiga da zasu iya biyan bukatun su

- Har ila yau, rahoton ya bayyana jihar da tafi kowace bashi a halin yanzu

Sakamakon wani bincike da wata kungiya mai rajin inganta zamantakewan al'umma mai suna BudgIT ta gudanar a shekarar 2017 ya nuna cewa jihohi 4 ne kawai a Najeriya ke iya biyan albashin ma'aikatan su ba tare da sun ciyo bashi ba.

Jihohin da binciken ya nuna suna iya biyan bukatun nasu dai sune jihohin Kano, Katsina, Rivers da kuma jihar Legas da ke kan gaba.

An kammala tatara sakamakon binciken ranar Alhamis amma sai rannan Juma'a aka fitar dashi bainar jama'a.

Jihohi 4 ne kawai ke iya biyan albashi ba tare da sun ciyo bashi ba a Najeriya
Jihohi 4 ne kawai ke iya biyan albashi ba tare da sun ciyo bashi ba a Najeriya

Abin da binciken yayi la'akari dashi shine jimlan kudaden shiga da jihohin suke samu a kowane wata da kuma kudaden da suke kashewa a kowane wata.

DUBA WANNAN: Abinda ya dace da Jonathan shine neman gafara daga Ubangiji da kuma 'yan Najeriya - APC

Har ila yau, binciken ya duba yanayin yadda jihohin ke karban haraji domin biyan basusukan da ake binsu. Jihar Osun itace tafi kowane jiha bashi a Najeriya domin binciken ya nuna cewa babu ingantatun hanyoyin tattara haraji a jihar.

Jihohin Kwara, Delta, Kebbi, Gombe da Ebonyi kuma suna kara inganta hanyoyin tattara harajin nasu wadda hakan na nufin a nan gaba zasu iya zama cikin jihohin da ka iya biyan bukatun su ba tare da ciyo bashin ba.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164