Za ayi nunin farko na sabon fim din da aka shirya na Sheikh Usman Dan Fodiyo a Bauchi

Za ayi nunin farko na sabon fim din da aka shirya na Sheikh Usman Dan Fodiyo a Bauchi

- Kamfanin I.M Productions zasu nuna sabon fim din da suka shirya na tarihin Sheikh Usman Danfodiyo

- An shafe tsahon shekara 14 ana shirya fim din

- Kamfanin ya kashe kudi Naira miliyan 80 wajen hada fim din

Wani kamfani mai shirya fina-finai mai suna I.M Productions ya sanar da cewa zasuyi nunin farko na fim din da suka shirya a kan babban malami Sheikh Usman Danfodio a jihar Bauchi.

Kamfanin sun shaida cewa an dau tsahoon shekara 14 ana hada shi wanda za a yi nunin sa na farko a gidajen kallo kafin a fara sayar da shi a kasuwa.

Masu hada fim din sun kai wa sarkin jihar Bauchi, Alhaji Rilwanu Sulaiman Adamu ziyara da shaida masa shirye-shiryen su na sakin fim din a Bauchi. Ali Babba, mai shirya fim din ya shaida dalilin su na zabar jihar Bauchi don a nuna fim dinne saboda muhimmiyar rawar da masarautar jihar ta taka a zamanin jihadin shugabancin Usman Danfodiyo.

Za ayi nunin farko na sabon fim din da aka shirya na Sheikh Usman Dan Fodiyo a Bauchi
Za ayi nunin farko na sabon fim din da aka shirya na Sheikh Usman Dan Fodiyo a Bauchi

A yayin da suke shirya fim din a shekarun da suke wuce sun kai ziyara ga marigayi Sarkin Musulmai, Alhaji Muhammad Maccido wanda ya nuna farin cikin sa game da shirya fim din.

Babba ya shaida inda suka ziyarta yayin hada fim din ya hada da sassan tarihi na jami’o’in Ahmadu Bello da ke Zaria, Usman Danfodiyo ta Sakkwato da jami’ar Bayero a Kano. Sun kara da kuma ganawa da manyan malaman tarihi don kara samun ingataccen bayani a yadda aka kafa tarihin muslunci.

Sun yi amfani da littafi mai suna Kifa’ul Mansur wanda Sultan Muhammad Bello ya wallafa wajen hada labarin fim din. Ya kuma shaida yadda suka fuskanci kalubale wajen hada fim din, musamman wajen samun fada domin kuwa yanzu babu irin su sai da suka gina tasu daga farko, da kuma koyawa ma’aikatan shirin don fim din ya tsaru sosai.

An kashe sama da Naira miliyan 80 a hada fim din ban da asarar wasu kayan gine-gine da suka yi da ruwan sama ya tafi da su.

DUBA WANNAN: Kamfanin Intels ya tuba, ya nemi gafarar gwamnati tare da alkawarin yin biyayya

Sarkin jihar Bauchi ya yaba da wannan shirin kayataccen fim da suka yi da cewar Ubangiji ne kawai zai saka musu don ba ‘yan Najeriya kadai fim din zai anfana ba har da mutanen Afirka da kewaye.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: